Rundunar ’yansandan Jihar Bauchi, ta kama wata mata mai shekaru 40 a duniya mai suna Fatima Ibrahim, mazauniyar Tashan-Jama’are, bisa zargin yin lalata da wani yaro ɗan shekara 12.
Rahotanni sun nuna cewa Fatima ta ɗauki yaron a matsayin mai taimaka mata a wajen sayar da ɗanwanke, a Tashan-Jama’are da ke ƙaramar hukumar Azare Katagum a Jihar Bauchi.
- Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Siyasantar Da Batun Asalin Cutar COVID-19
- Manchester United Na Zawarcin Matheus Cunha Na Wolves
Har ila yau, an bayyana cewa yaron wanda almajiri ne, yana zaune a gidan matar inda ake zargin ta yi lalata da shi na tsawon watanni biyu.
Kakakin rundunar ’yansandan jihar, CSP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Talata.
“A yayin bincike, yaron ya bayyana yadda ya ɗauki matar tamkar uwa a gare shi, amma ta riƙa aikata abubuwan da suka saɓa da tarbiyya, musamman idan babu mutane,” in ji Wakil.
“Yaron ya kuma ce akwai lokacin da ta ba shi wani lemun tsami da yake zaton an saka wani abu a ciki kafin abin ya faru. Ya bayyana cewa ta sha maimaita wannan aika-aikar a kansa,” Wakil ya ƙara da bayani.
Wakil ya ce a yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da shi.
Ya ce za a ci gaba da tantance bayananta, sannan a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp