Rundunar ‘yansandan Jihar Gombe, ta karyata wasu rahotannin da ke cewar ta kama ‘ya’yan wata jam’iyya a jihar kan dangwale takardun jefa kuri’a kafin zabukan gwamoni da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi a ranar Asabar.
Kakakin rundunar, Mahid Muazu Abubakar ne, ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a yau Juma’a.
- Sin Ta Samu Jarin Waje RMB Yuan Biliyan 268.44 A Watanni 2 Na Farkon Bana
- Jama’ar Kano Sun Shirya Fita Zabe Duk Da Rade-Radin Samun Tashin Hankali
Ya ce, jam’iyyar da ake magana a kai, ta wayar da kan ‘ya’yanta ne kan yadda za su kada kuri’ar don guje wa lalata takardun zabe, inda ya kara da cewa, labaran da kafafen na sada zumunta suka wallafa karya ce tsagwaronta.
A cewarsa, bisa binciken da rundunar ta gudanar ta gano cewa, jam’iyyar ta yi amfani da takardun ne a matsayin gwaji ga ‘ya’yanta kan yadda za su jefa kuri’arsu, inda kuma kakakin ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi watsi da rahoton na karya wanda kuma bai da wani tushe bare makama.
Rundunar ta kuma gargadi al’ummar jihar da su gujewa yada bayanan da ba su tantance sahihancinsu ba.