Rundunar ‘yansandan jihar Benuwe ta yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga biyu a Karamar Hukumar Katsina-Ala da ke jihar tare da kwato makamai.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa a ranar Laraba, mai dauke da sa hannun kakakin rundunar, SP Sewuese Anene.
- Sojoji Sun Wanke Fursunoni 200 Da Ake Zargin Alaka Da Boko Haram A Borno
- Zargin Hannu A Ta’addanci: Gwamnatin Tarayya Ta Gayyaci Sheikh Gumi Domin Amsa Tambayoyi
A cikin sanarwar, Anene ya ce, rundunar ‘yansandan ta kashe ‘yan bindigar a kauyen De-Mtsa, Kastina-Ala, bayan artabu da suka yi.
A cewarsa, wata tawaga ta Operation Zenda Joint Task Force (JTF) karkashin jagorancin Kwamandansu, ASP Felix Nomiyugh, ta kutsa yankin tare da kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar yayin wani kazamin artabu.
“Bayan kashe su mun kwato bindiga kirar 06 guda daya, harsashin AK-47 guda uku, wasu alburusai 80, sai kuma wayoyin hannu da sauransu,” in ji kakakin.
Sanarwar ta kara da cewa, Kwamishinan ‘yansandan, Mista Emmanuel Adesina, ya yaba wa jami’an bisa jajircewar da suka nuna.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su rika tallafa wa ‘yansanda da bayanai masu inganci domin dakile ayyukan ta’addanci a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp