Rundunar ‘yansandan jihar Kebbi ta ce jami’anta a karamar hukumar Shanga sun kashe wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da sanyin safiyar Lahadi.
Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 2:30 na sanyin safiyar Lahadi, ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu cewa an hangi wasu gungun masu garkuwa da mutane a dajin da ke kan hanyar Tungargiwa zuwa Saminaka, inda ake zargin suna shirin kai wa matafiya da ke kan hanyar hari ne.
- Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP
- Trump Ya Ce Zai Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganawa Da Putin Da Zelensky Lokaci Guda
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, CSP Nafi’u Abubakar ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, da samun rahoton, babban jami’in ‘yansanda na shiyyar Shanga ya yi gaggawar tara tawagar ‘yansanda da ‘yan banga zuwa wurin.
Sanarwar ta kara da cewa, “Da isar rundunar, ta fara artabu da ‘yan bindigar, inda ta samu nasarar kashe Uku, tare da kwato bindiga kirar AK-47,” in ji sanarwar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Kebbi, CP Bello M. Sani ya yabawa babban jami’in da jami’ansa bisa wannan namijin kokarin da suka yi. Ya bayyana nasarar a matsayin shaida na kudurin rundunar na kawar da masu aikata munanan laifuka a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp