Rundunar ‘yansandan jihar Kaduna ta ce, biyo bayan samun bayanan sirri kan wasu ‘yan ta’adda, rundunar ta yi nasarar cafke mutane 13 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, inda ta kashe hudu daga cikinsu a wurare daban-daban a yayin musayar wuta.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO), ASP Mansir Hassan, ya ce, rundunar ta samu gagarumar nasara a yayin musayar wutar inda ta kwato makamai da kayayyaki daban-daban.
Abubuwan da aka kwato sun hada da; Bindigogin AK47 guda 2, Bindigar (revolver) kirar hadin gida guda uku, Babura 2, Alburusai guda 115, Bindigu kirar gida guda hudu, Buhunan tabar wiwi guda uku da kuma wayoyin hannu guda uku.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Musa Yusuf Garba, ya yabawa jami’an, kuma ya yi kira ga jama’a da su rika kai rahoto ga ‘yansanda ko duk wani jami’in tsaro da ke kusa da su game da duk wani mutum ko kungiya da ke da alaka da kungiyar ta’addanci.