Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce, ta samu nasarar kubutar da mutum hudu daga hannun masu garkuwa da kuma kama mutum 17 da ake zargi da hannu dumu-dumu a wajen aikata laifin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.
Ya ce, an kama wadanda ake zargin da laifin garkuwa da mutane har sau uku cikin wata daya, sakamakon kokarin da rundunar ‘yansandan jihar Kanon ke yi na kakkabe bata-gari daga cikin al’umma.
Kamar yadda daya daga cikin wadanda aka Kaman ya ce, abu na farko ya faru ne lokacin da wata motar haya ke tawo wa daga karamar hukumar Funtuwa, ta nufi jihar Kebbi, wasu masu garkuwa suka kama shi, suka rike shi, har tsawon kwana 12; sai da aka biya kudin fansa sannan suka sake shi.
An kama wanda wadanda ake zargin ne a tashar Rijiyar Zaki, da ke Kano, lokacin da suke kokarin hawa mota su gudu Faskari.
SP Kiyawa ya ce, yanzu haka suna ci gaba da bincike, kuma suna samun bayanai da za su taimaka musu wajen kamo sauran wadanda ke da hannu a kan wannan laifin.
Aboda haka, sai kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya bukaci al’umma sy ci gaba da ba su hadin kai domin ganin an kawo karshen masu aikata miyagun laifuka a fadin jihar ta Kano.