Rundunar ‘yansandan jihar Filato ta ce, ta samu nasarar ceto Injiniya Alexander Plangnan, babban sakataren dindindin na ma’aikatar ayyuka ta jihar daga hannun masu garkuwa da mutane wadanda suka saceshi tare da motar ofis kira Hilux a kofar gidansa da ke rukunin gidaje na State Low-cost da ke Jos ta arewa.
Wasu masu garkuwa da yawansu ya haura hudu dauke da makamai ne suka sace shi.
A wata sanarwar da Kakakin hukumar (PPRO), DSP Alfred Alabo, ya ce, cikin gaggawa da suka samu labarin garkuwar, babban jami’in ‘yan sanda na caji ofis din Rantya, SP Ayuba Iliya ya ziyarci wajen tare da tawagarsa gami da kaddamar da bincike.
Ya kara da cewa bisa aikin hadin guiwa tsakanin ‘yansandan caji Rantya da Jengre tare da sashin dakile masu garkuwa da mutane na Shalkwatar ‘yansandan Filato ne suka ceto shi da motar a kauyen Mistali da ke karamar hukumar Bassa.
Ya ce, suna ta kokarin cafko mutanen domin dakile aikace-aikacen masu garkuwa da mutane.
SP Alabo ya roki jama’a da suke taimaka wa ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro da bayanai domin tabbatar da an dakile duk wata motsin ‘yan ta’adda a fadin jihar.