Jami’an rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya Abuja sun ceto wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Promise Eze, bayan da wani mutum da ta hadu da shi a wani dandalin sada zumunta na intanet ya daure ta ya bar ta a sume.
Wanda ake zargin da aka bayyana sunansa da Michael Prince amma daga baya ya bayyana sunansa na gaskiya da Emmanuel Okoro, yanzu haka ya tsere, kuma ‘yansanda sun kaddamar da farautarsa domin tabbatar da cafke shi cikin gaggawa.
- Mata Mu Tsaya Da Kafafunmu Kar Mu Tsaya Sai An Bamu – Khadeejah Abdullahi
- Me Ke Kawo Saurin Talaucewa Bayan Kammala Aikin Gwamnati?
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan, Josephine Adeh, ta fitar, ta ce ‘yansandan sun samu kiran gaggawa daga wani otal da ke unguwar Wuse a cikin Babban Birnin Tarayya Abuja bayan sun lura da wasu abubuwa da ake zargi a daya daga cikin dakinta.
Adeh ta ce da isowar jami’anta ne suka gano Eze daure a kan wata karamar kujera da bakinta a manne da filasta, kuma tana kwance a kasa a sume.
Ta lura cewa nan take aka garzaya da Eze asibitin gundumar Wuse, inda aka taimaka wajen farfado da ita.
“Da sauri jami’an ‘yansanda suka isa wurin, inda suka gano wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Promise Eze, ‘yar Jihar Ebonyi, daure a wata karamar kujera an rufe bakinta da filasta. An same ta a sume kuma cikin damuwa. Jami’an ‘yan sanda sun dauki matakin gaggawa, inda suka kubutar da ita daga hannun wadanda aka yi garkuwa da su, sannan suka garzaya da ita asibitin gundumar Wuse, inda ta farfado,” in ji sanarwar.
Adeh ta ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa Eze ta leka otal din a safiyar ranar 30 ga watan Janairu tare da Okoro, wanda ta hadu da shi ta intanet.
A cewarta, wanda ake zargin ya gabatar da kansa a matsayin ma’aikacin kamfanin mai da ke Jihar Delta.
Adeh ta bayyana cewa tun da farko wanda ake zargin ya gayyaci Eze ta ziyarce shi a Jihar Delta amma ta ki amincewa da hakan amma ta amince ta same shi a Abuja a maimakon haka.
“Bincike na farko ya nuna wani yanayi na yaudara da tashin hankali, ta shiga otal ne kwana daya da ta gabata, a ranar 30 ga watan Janairu, 2025, da misalin karfe 7:00 na safe, tare da wani mutum da ya bayyana sunansa da Emmanuel Okoro daga Jihar Legas.
“Sai dai yayin da ‘yansanda ke mata tambayoyi, matar da aka cutar ta bayyana cewa ta hadu da wanda ake zargin a intanet, inda ya gabatar da kansa ga Michael Prince, inda ya ce shi ma’aikacin kamfanin mai ne da ke Jihar Delta.”
Adeh ta kara da cewa Eze ya ce Okoro ya fid da wuka don yi mata barazana kafin ya daure ta ya manne bakinta a cikin bandakin otal din.
Adeh ta ce kwamishinan ‘yansandan Babban Birnin Tarayya Abuja, CP Olatunji Disu, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin tare da shawartar ‘yanmata kan illar haduwa da baki ta intanet ba tare da taka tsantsan ba.