Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta samu nasarar cafke motoci bakwai da aka sace tare da taimakon na’urar rajistar motoci ta yanar gizo (e-CMR).
Motocin da aka sace daga jihohi daban-daban, an yi nasarar mayar da su ga masu su.
- An Haramta Wa Tankokin Man fetur Da Ke Jigilar Lita 60,000 Zirga-zirga A Faɗin Titunan Nijeriya
- Jakadan Sin Dake Najeriya Ya Gana Da Karamar Ministar Harkokin Wajen Kasar
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce an bi diddigin motocin da aka sace tare da kwato su a jihohi daban-daban da suka hada da Kano, Kogi, da Abuja.
Ya ce, motocin da aka kwato sun hada da wata farar mota kirar Howo, wacce aka sace daga Riruwai, karamar hukumar Doguwa, Kano, a ranar 17 ga watan Janairu, 2025, aka kuma gano ta a Lokoja, jihar Kogi.
Akwai wata bakar mota kirar Honda Accord 2013, wacce aka sace daga Abuja ranar 18 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a filin jirgin sama na Kano.
Bugu da kari, akwai wata farar mota kirar Mercedes Benz GLK wacce aka sace a hanyar Magwan Kano a ranar 27 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a Hotoro Quarters Kano da wata jar Toyota Corolla LE da aka sace a Abuja a ranar 30 ga Janairu, 2025, aka gano ta a Kano.
Daya kuma wata bakar mota kirar Toyota Camry, wacce aka sace a Kaduna ranar 27 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a Kano.
Akwai Wata farar Toyota Hilux da aka sace daga Katsina a ranar 15 ga Fabrairu, 2025, aka same ta a Ring Road Bypass, Kano.
Har ila yau, akwai wata bakar mota ash mai suna Pontiac Vibe, wacce aka sace daga Katsina a ranar 15 ga Fabrairu, 2025, kuma aka gano ta a Ring Road Bypass, Kano.
Rundunar ‘yansandan ta jaddada mahimmancin rajistar motoci a na’urar e-CMR wajen bin diddigin motocin da aka sace, inda ta bukaci masu abin hawa da su yi rajista ta shafin https://cmris.npf.gov.ng don inganta tsaro.
Rundunar ta kuma ja hankalin jama’a da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da bayar da rahoton duk wani abu da suka shakku akai.