Rundunar ‘Yansandan jihar Ribas ta tabbatar da mutuwar mutane 12 a wani harin bam da ya afku a wata haramtaccan wurin hako danyen mai a unguwar Rumuekpe da ke karamar hukumar Emohua a jihar.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, lamarin ya afku ne da misalin karfe 2:00 na rana a wurin wani bututun mai da ya ratsa ta cikin al’umar yankin Neja Delta.
- riMataimakiyar Wike Ta Lashe Zaben Sanatan Ribas Ta Yamma
- ‘Yansanda Sun Cafke Jami’ansu 4 Kan Zargin Yin Magudin Zabe A Ribas
Wani tartsatsin wuta ya fito daga wata motar safa da take makare da danyen mai domin jigilar kayayyaki zuwa matatun mai, lamarin da ya haifar da wuta da fashewar abubuwa.
Rundunar ‘yan sandan, a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Fatakwal ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawunta, Grace Iringe-Koko, ta ce wadanda harin ya rutsa da su, wadanda har yanzu ba a san ko su waye ba, sun mutu ne a lokacin da suke diban mai daga wajen.
Iringe-Koko ya bayyana cewa, kimanin motoci biyar da babura masu kafa uku guda hudu da babur daya duk sun kone yayin fashewar bam din.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta tabbatar da fashewar bututun mai a yankin Rumurkpe da ke karamar hukumar Emuoha ta jihar Ribas.