‘Yansanda sun tura Shuaibu Alhaji Yushau, wanda ya hau karfen gidane rediyo a yankin Katampe da ke Abuja domin kashe kansa a ranar Litinin saboda matsin rayuwa, zuwa gidan mahaukata domin duba lafiyarsa.
‘Yansanda sun tsare Yushau a babban birnin tarayya, bayan an yi nasara ya sauko daga kan karfen gidan rediyon da yau da nufin hallaka kansa.
- Adadin Wadanda Suka Mutu A Yakin Gaza Da Isra’ila Ya Kai 38,000
- Rikicin Masarautar Kano: Tinubu Da Sanusi II Suna Da Alaka Mai Karfi – Fadar Shugaban Kasa
Ganau, ya bayyana cewar matakin da Yushau ya dauka ya haifar da rudani a yankin.
An sanar da ‘yansanda lamarin, abin da ya sa suka yi gaggawar zuwa wajen tare da tattaunawa da shi har ta kai ga ya sauko.
Kakakin ‘yansandan babban birnin tarayya, SP Josephine Adeh, a ranar Talata ta bayyana cewar za a gudanar da shi tare da tuhumarsa kan kokarin aikata kisan kai.
Idan ba a manta ba LEADERSHIP ta ruwaito yadda matashin ya haifar da rudani bayan ya hau karfen gidan rediyon tare da kokarin fadowa kasa.
Matashin ya ce ya yi yunkurin kashe kansa ne sakamakon tsadar rayuwa da ake fuskanta da kuma kokarin ceto ‘yan Nijeriya daga halin da suke ciki.