Rundunar ’Yansandan Nijeriya ta tura jami’ai na musamman don haɗa kai da sojoji da ‘yan sa-kai wajen nemo ɗaliban da aka sace a makarantar Government Girls Comprehensive Secondary School, Maga da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi.
Kakakin rundunar, CSP Nafiu Abubakar Kotarkoshi, ya ce tawagar na bincike a hanyoyin da ’yan bindiga suka bi da dazuzzuka domin ceto ɗaliban tare da kama waɗanda suka kai harin.
- Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba
- Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%
A cewar ’yansanda, a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 4 na asuba, wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai suka kutsa makarantar, suna harbe-harbe.
’Yansanda da ke wajen sun yi artabu da su, amma ’yan bindigar sun tsallaka katangar makarantar tare da sace ɗalibai 25.
Sun kashe wani mutum mai suna Hassan Makuku, tare da jikkata wani Ali Shehu.
Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kebbi, CP Bello Sani, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu.
Ya kuma yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu, su kasance masu lura, su kuma ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro.














