A halin yanzu dai kokarin da aka fara yi na tsawon shekaru ya haifar da da mai ido, bayan da aka kaddamar da fara hakar man fetur na farko a yankin Arewacin Nijeriya, inda kamfanin ‘Kolmani Integrated Debelopment Project’ ya jagoranjci hakar Man a yankin Kolmani da ke karamar hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.
Yankin na Kolmani ya kasance ne a tsakanin jihohin Gombe da Bauchi a tsakiya yankin Arerwa maso gasashin Nijeriya. Wannann kuma yana faruwa ne bayan shekara 63 da aka gano tare da fara hakar Mai a yankin Oloibiri, na Jihar Bayelsa.
- Jirgin C919 Na Kasar Sin Ya Samu Amincewar Kara Kera Shi
- Hadin Gwiwa Tsakanin Matasan Sin Da Afirka Zai Fadada Cin Gajiyar Kasashen Su
Fara hakar Man da aka yi a halin yanzu, Nijeriya na fatan samun gangar Mai fiye da Biliyan daya a karon farko cikin Man da aka yi kiyasin yana nan ajiye a yankin na Kolmani ana kuma sa ran za a iya kai ga samun gangar mai fiye da Biliyan 19 idan aka cigaba da bincike da kuma gano karin Man da Allah ya ajiye a karkashin kasa a yankin gaba daya. Ana kuma sa ran Nijeriya za ta ci gajiyar ‘Cubic’ Biliyan 500 na iskar gas a matakin farko na hakar Man fetur din da aka fara.
Masana sun bayyana cewa, za fara hako gangar Mai 50,000 a kullum a karon farko daga nan kuma sai a kara gaba zuwa akalla ganga Biliyan 1 wanda haka kuma zai kai Nijeriya zuwa samun gangan mai Biliyan 38 in aka hada gaba daya abin da Nijeriya za ta rinka samarwa a kullum.
Wannan nasarar ta zama abin marhabin ba wai a yankin Arewa kadai ba har ma a fadin tarayyar Nijeriya gaba daya. Babban dalilin haka kuma shi ne yadda wannan albarkar kasar ta zama wata kafa na kwakulular tattalin arzikin al’ummar Nijeriya ba tare da an samar da cikakken cigaba ba, wannan abin takaici ne don kuwa ba haka abin yake ba a wasu kasashen duniya.
Tuni dai, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yayin kaddamar da aikin hakar Man ya sanar da cewa a halin yanzu har an samu zuba jari na fiye da dala Biliyan 3 duk kuwa da rashin cikakken tagomashi da bashi a bangaren a halin yanzu.
Abin alkharin a halin yanzu shi ne masu gudanar da harkokin albarkatun Man kasar nan sun dauki darasin da ya kamata a kan yadda za su gudanar da batun haka da saffara Man fetur ta yadda al’ummar da ke zaune a yankin da ake hakar Man fetur din za su amfana yadda yakamata, abin nufi a nan shi ne kada a sake kwatanta yadda hakar albarkatun Man fetur ya zama masifa ga al’ummar yankin Neja Delta.
Haka kuma akwai rahoton da ke nuna cewa, wasu manyn mutane a Nijeriya sun fara gargadin cewa lallai a kula don kada a yi lalata muhalli kamar yadda ake samu a wurare da dama inda ake hakar Man fetur a duniya.
Akwai kuma rahoton da ke nuna cewa kamfanin Mai na NNPCL ya shirya samar da matatar Mai, da kamfanin samar da iskar gas da kamfanin wutar lantarki mai karfin meghawatt 300 za kuma a samar da kamfanin samar da takin zamani wanda zai rinka samar da buhu 2,500 a kullum.
A ra’ayin wannan jaridar, in har aka samu nasarar cimma wadannan abubuwan da aka zayyana, zai kai ga bunkasa tattalin arzkin kasa ta hanyoyi masu yawa tare da samar da ayyukan yi ga dimbin ‘yan Nijeriya wanda hakan kuma zai kai ga taimakawa wajen bayar da gudunmmawar karin kudaden shiga na kasa wato ‘GDP’.
Tabbas akwai wasu da suke dari-dari an kan babu wasu abubuwan da za su canza daga abin da ake gani a yankin Neja Delta a halin yanzu, sauran al’ummar kasa ba su amfana yadda yakamata ba daga abin da ake samu a bangaren Man fetur. Ga wadannan ‘yan Nijeriya suna buga misali ne da yadda talauci ya mamaye yankin, abubuwa duk sun tabarbare, ga yawaitar matasa marasa aikin yi duk wadanan na kasancewa duk da Mai a Nijeriya, wanna ya sa ake tunanin ko samun Man fetur ya kasance kamar tsinuwa ne ga Nijeriya don rayuwa ta fi inganta kafin da aka ga gano Man fetur da aka yi da a halin da aka gano Man fetur din.
A kwanakin baya ne wata hukumar gwamnati ta sanar da cewa, a akwai wasu ‘yan Nijeriya fiye Miliyan 133 da ke rayuwa a cikin talauci. Tunda farko kuma wasu kasashen duniya sun bayyana Nijeriya a matsayin babbar hedikwatar talauci ta duniya. Wannan kuma yana faruwa ne duk da cewa, Nijeriya ce ta 8 a cikin kasashen da ke samar da Man fetur a duniya. Sun kuma nuna yadda ake da matatun mai masu yawa a kasar amma duk a banza, don har yanzu Nijeriya na shigo da albarkatun Man ne daga kasashen waje don amfanin al’ummar ta. A kan wadannan dalilan ne al’umma da dama ke nuna damuwarsu a kan abin da zai iya faruwa da samun man fetur a yankin Arewa.
A ra’ayin wannan jaridar babu wani abin da za a yi wa murna ta gano Man fetur a Arewancin Nijeriya. Wadanan dai da suka yi babakere wajen tafiyar da harkokin Mai a kasar nan tun da aka fara gano Man shekara 63 da suka wuce, sune daii za su cigaba da tafiyar da wannan ma da aka gano a arewacin Nijeriya, sune suka hana ‘yan Nijeriya samun cikakken amfanin alhairan da ake sdamu daga Man fetur din, wanda talaucin da ke bayyane a tsakanin ‘yan Nijeriya bai kamata a ce ba, Nijeriyan na daga cikin kasashe masu samar da Man fetur ba a duniya.
Idan zamu kwatanta wasu kasashe da albarkatun Man fetur din su bai ma kai wanda Allah ya bamu ba, amma masu tafiyar da harkokinj kasar tasu sun tabbatar da al’ummar kasar na amfana da abin da ake samu yadda ya kamata ta hanyar inganta harkokin rayuwar al’ummar su. Ana samar da Man fetur a kasashen a farashin da ya yi daidai dana duniya ba tare da wata matsala ba.
Har yanzu muna fuskantar satar albarkatun man fetur, wanda ake zargin masu hannu da shunine wadanda suke da abokan harkarsu a kasashen waje, irin wadanan mutane nadanda suna jira don fara gani albarkatun man da za su fito daga Kolmani.
Duk da wadanna matsalolin da ake hangowa, muna fatan wadanda jami’an gwamnati da dukkan wadanhda suke jagorantar al’amarin hako Mai na Kolmani za su ba marada kunya ta yadda Nijeriya za ta amfana da wannan damar da aka samu. Musamman ganin yadda al’umma ke murnar samun mai a Arewacin Nijeriya.