Ana zargin wasu makiyaya sun kashe mutane 15 a yankunan Ogwumogbo da Okpo’okpolo na ƙaramar hukumar Agatu dake jihar Benuwe.
Majiyoyinmu sun bayyana cewa waɗanda aka kashe sun kasance ‘yan kasuwa ne da ke dawowa daga kasuwar Oweto a Agatu lokacin da maharan suka fito daga daji suka harbe su, inda suka kashe 15 nan take.
- An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya
- Ƙungiyar Fulani Makiyaya Ta Nuna Damuwarta Na Ɓacewar Mataimakin Shugabanta
Tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Agatu, John Ikwulono, ya tabbatar da harin da aka kai wa ‘yan kasuwar a ranar Asabar da yamma, inda ya bayyana cewa maharan sun kwace kuɗaɗe da kayayyakin waɗanda aka kashe kafin su gudu cikin daji.
“Har yanzu wasu mutane sun ɓace ba a same su ba, yayin da waɗanda suka jikkata an kai su wani asibiti a yankin,” in ji Ikwulono.
Kakakin Ƴansandan jihar, Catherine Anene, ta ce har yanzu ba a sanar da ita cikakken bayani kan lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp