Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na neman bashi daga ƙasashen waje da ya haura dala biliyan 21 domin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 zuwa 2026.
Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ababen more rayuwa, da tsaro, da noma da kuma gina ɗan Adam.
- Majalisar Dattawa Za Ta Yi Zama Na Musamman Don Karrama Buhari
- Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro
Da yake gabatar da rahoton a zauren majalisa yau Talata, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan basussukan cikin gida da na waje, Sanata Aliyu Wamako, ya ce an jinkirta amincewar rahoton ne saboda hutu na majalisa da kuma jinkiri wajen samun takardun daga Ofishin Kula da Basussuka (DMO).
Bashin da aka amince da su sun haɗa da:
Dala biliyan 21.19 na bashin kai tsaye daga ƙetare
Yuro biliyan 4
Yen biliyan 15 (na Japan)
Tallafin dala miliyan 65
Kuma aron cikin gida ta hanyar sayar da hannun jarin gwamnati (bond) na kusan Naira biliyan 757.
Har ila yau, akwai shirin tara kuɗi har dala biliyan 2 ta hanyar takardun lamuni da za a fitar cikin ƙasa amma a kuɗin ƙetare.
Shugaban kwamitin kasafi, Sanata Olamilekan Solomon, ya ce wannan amincewa tsarin doka ce kawai, domin an riga an haɗa bashin cikin tsare-tsaren kasafin kuɗi da MTEF tun da farko.
Sanata Sani Musa (Niger Ta Gabas) ya bayyana cewa wannan shiri ba na shekara ɗaya ba ne, amma zai shafi rabon kuɗi na tsawon shekara shida, yana mai jaddada cewa Nijeriya ba ta taɓa gazawa wajen biyan bashinta ba.
Shugaban kwamitin Bankuna da harkokin kuɗi, Sanata Adetokunbo Abiru (Lagos Ta Gabas), ya tabbatar da cewa dukkan bashin na bin ƙa’idojin dokar kula da bashi da ta ɗabi’un da suka dace da dokar kuɗi.
Sai dai Sanata Abdul Ningi (Bauchi Ta Tsakiya) ya nuna damuwa game da ƙarancin bayani da ake da shi kan yadda za a raba bashin da kuma hanyoyin da za a biya su.
Ya nemi a bayyana adadin da kowace jiha ko hukuma za ta samu, da kuma amfanin bashin domin a iya bayyana wa al’umma gaskiya.
A cikin jerin ayyukan da za a aiwatar da kuɗin akwai:
Gina layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri
Tsarin wutar lantarki da sadarwa na zamani
Harkokin tsaro
Noma da aikin gidaje
Sanata Victor Umeh (Anambra Ta Tsakiya) ya goyi bayan shirin, yana mai bayyana cewa wannan ne karon farko da ake ware dala biliyan 3 domin gina layin dogo a gabashin Nijeriya.
Mataimakin Shugaban Majalisa, Barau Jibrin ya yabawa kwamitin bisa aikin da ya yi, yana mai cewa “dukkan yankunan ƙasa na cikin shirin kuma hakan na nuna cewa Agenda ta ‘Renewed Hope’ tana aiki.”
Majalisar ta jaddada cewa duk wani kuɗin da za a fitar dole ne a yi amfani da shi ne kawai wajen ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma, bisa tanadin dokar kuɗin gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp