Jam’iyyar PDP ta yi barazanar kin amincewa tare da yin watsi da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 da aka tattara zuwa yanzu a cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja.
Babbar jam’iyyar adawa ta kasar ta yi ikirarin cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gaza sanya sakamakon zaben daga Jihohi a tashar IReV da kuma kan allo a Cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa (NCC).
Wakilin jam’iyyar PDP (Agent) a wajen amsar sakamakon zaben shugaban kasa, Sanata Dino Melaye, ya daga jijiyar wuyarsa ne kan sakamakon zaben shugaban kasan da ya zo daga jihar Kwara.
Melaye ya yi adawar cewa APC ta gaza hanzarta daura sakamakon zaben daga rumfunan zabe a yanar gizo da suka amsa, don haka ya ce akwai ayar tambaya a sakamakon.
Kodayake, shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, wakilai na Jam’iyyu sun riga sun amince da sakamakon zaben jihar Kwara kuma har sun sanya hannu a matakin gundumomi da jihar.
Yakubu ya ce doka ba ta bukaci a yi hada-hada kan sakamakon da aka dora ba, sai dai bisa sakamakon da aka tattara a kananan hukumomi da jihohi.