Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), Ambasada Haruna Zago, ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Wani ma’aikacin hukumar ya tabbatar da rasuwar Haruna Zago a asibiti, inda ya bayyana cewa marigayin ya kwanta rashin lafiya na wani lokaci kafin rasuwarsa.
- Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
- Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano
Haruna Zago ya kasance Shugaban Hukumar REMASAB tun ranar 5 ga watan Yuli, 2023, bayan naɗin da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi masa.