Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) da Kungiyar Kananan Ma’aikata (NASU), sun dakatar da yajin aikin da suke yi bayan wata ganawa da suka yi da ministan ilimi, Adamu Adamu a Abuja, a ranar Asabar.
Ana sa ran dakatarwar za ta fara aiki daga ranar Laraba.
- Da Dumi-Dumi: An Kori Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Enugu Daga Jam’iyyar
- Zan Tsamo Nijeriya Daga Matsalar Rashin Wutar Lantarki – Atiku
A cewar Ministan Ilimin, Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 50 don biyan alawus-alawus ga mambobin SSANU da NASU da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).
Sai dai ayyuka za su takaita a jami’o’in gwamnati sakamakon yajin aikin da ASUU ke ci gaba da yi.