Shugaban kasa, Bola Tinubu ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa da sakataren jam’iyyar mai mulki, Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Iyiola Omisore, ranar Talata a fadar shugaban kasa, Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa, Adamu da Omisore sun ajiye mukamansu ne a farkon makon da ya gabata, gabanin taron majalisar zartarwa ta jam’iyyar ta kasa da aka shirya gudanarwa a ranakun Litinin da Talata 18 da 19 ga watan Yuli.
Duk da cewa, a hukumance ba a tabbatar da dalilin ziyarar da tsoffin shugabannin suka kawo ba, amma ana kishi-kishin cewa, ba zata rasa alaka da kokarin warware matsalolin da suka dabaibaye shugabancin jam’iyyar ba.
A lokacin da ake ta yada jita-jita game da murabus dinsu, an samu labarin cewa, tsohon shugaban jam’iyyar, Adamu, ya ce ba zai yi wani tsokaci kan dalilin murabus dinsa yanzu ba har sai Shugaba Tinubu ya dawo kasa daga birnin Nairobi na kasar Kenya a lokacin.