Tobi Amusan wacce ta ciwo wa kasar Nijeriya tagulla a wasan tsare na gudun mita 100 a gasar wasannin Commonwealth, ta shiga cikin jerin sunayen mata ‘yan wasa na duniya da za a karrama da lambar yabo ta shekarar 2022.
Amusan ta shiga gaban sauran mata ‘yan tsaren inda ta samu maki 12 a gasar.
Amusan ‘yar shekara 25 da haihuwa, a yanzu haka ita ce zakara a gasar wasan ta duniya ta Diamond League da gasar wasanin Commonwealth a gasar tsare ta mata na mita 100.
‘Yar wasan za ta kuma fafata da takarorinta mata ‘yan wasa kamar su, Selly-Ann Fraser-Pryce, Kimberly Garcia, Sydney McLaughlin da kuma Yulimar Rojas domin samun lambar yabon wacce za a sanar a cikin watan Disambar wannan shekarar.