• English
  • Business News
Sunday, May 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yar Nijeriya Ta Zama Birgediya-Janar Din Sojin Amurka

by Sadiq
3 years ago
in Labarai
0
‘Yar Nijeriya Ta Zama Birgediya-Janar Din Sojin Amurka
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wata soja ‘yar asalin Nijeriya, Amanda Azubuike ta samu karin girma daga mukamin Laftanar-Kanar zuwa Birgediya-Janar na Sojin Amurka a sansanin soji da ke Fort Knox, Kentucky, a Amurka.

Azubuike, haifaffiyar Landan wadda mahaifanta ‘yan Nijeriya ne, ta shiga aikin sojan Amurka a 1994, inda ta zama jami’a a fannin jirgin sama bayan ta kammala kwas din tukin jirgin sama a Kwalejin Koyon Tukin Jirage ta Sojoji.

  • Da Dumi-Dumi: An Harbi Tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan 
  • Kammala aikin tashar ruwa mai zurfi ta Lagos zai ingiza bunkasar tattalin arzikin Najeriya

A cikin sakon taya murna a shafin Twitter, Manjo-Janar Antonio Munera ya ce: “Ina taya murna ga sabuwar USACC da ta samu ci gaba @dcg_armyrotc, Birigediya-Janar Amanda Azubuike! A yau, ta karbi tauraruwarta ta 1 daga Janar James Rainey, @armyfutures, yayin wani biki tare da dangi, abokai, da shugabannin al’umma.

Azubuike ta yi aiki a matsayin mataimakiyar kwamandan rundunar sojin Amurka ta Cadet kuma a baya ta zama Babbar Hafsan Hafsoshi da Babbar Mai Bada Shawara kan Soja a Ofishin Sakataren Tsaro.

Ta kuma kasance Shugabar Hulda da Jama’a a Kudancin Amurka, a yankin Fort Lauderdale, da Daraktar Hulda da Jama’a, Hadin gwiwar Rundunar HQs-‘National Capital Region/Military District ta Washington DC.

Labarai Masu Nasaba

Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF

Budurwa ƴar shekara 15 Ta Jefar Da Jariri A Sansanin Ƴan Gudun Hijira A Borno 

Ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara ta sadarwa don kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta kasa da kuma ma’aikaciyar Hulda da Jama’a ta kungiyar NFL, Washington Redskins.

Azubuike ta na da digiri na farko a Kimiyya a harkar sadarwa da ilimin kafafen yada labarai a Jami’ar Central Arkansas, Jagoran Fasaha a Tsaron Kasa da Nazarin Dabaru daga Kwalejin Yakin Sojin Amurka, kuma Jagora ce ta Nazarin Kwararru, Hulda da Jama’a da Sadarwar Kasuwanci daga Jami’ar Georgetown.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 'Yar NijeriyaAmurkaJanarSoji
ShareTweetSendShare
Previous Post

Da Dumi-Dumi: An Harbi Tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan 

Next Post

An Fara Rangadin Nuna Kashi Na Uku Na Fina-Finan Kasar Sin A Afirka

Related

Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF
Labarai

Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF

7 hours ago
Budurwa ƴar shekara 15 Ta Jefar Da Jariri A Sansanin Ƴan Gudun Hijira A Borno 
Labarai

Budurwa ƴar shekara 15 Ta Jefar Da Jariri A Sansanin Ƴan Gudun Hijira A Borno 

13 hours ago
NNPCL Ta Rufe Matatar Mai Ta Fatakwal
Labarai

NNPCL Ta Rufe Matatar Mai Ta Fatakwal

13 hours ago
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mazauna Kauyuka 4 A Taraba Bayan Taron Zuba Jari
Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mazauna Kauyuka 4 A Taraba Bayan Taron Zuba Jari

14 hours ago
Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar
Rahotonni

Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar

17 hours ago
Za Mu Ci Gaba Da Aikin Neman Man Fetur Arewacin Nijeriya — Ojulari
Labarai

Za Mu Ci Gaba Da Aikin Neman Man Fetur Arewacin Nijeriya — Ojulari

20 hours ago
Next Post
An Fara Rangadin Nuna Kashi Na Uku Na Fina-Finan Kasar Sin A Afirka

An Fara Rangadin Nuna Kashi Na Uku Na Fina-Finan Kasar Sin A Afirka

LABARAI MASU NASABA

An Gano Kofin Gasar Zakarun Turai Na Mata Bayan Sace Shi Da Aka Yi

An Gano Kofin Gasar Zakarun Turai Na Mata Bayan Sace Shi Da Aka Yi

May 24, 2025
Firaministan Sin Ya Sauka A Indonesia Domin Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Sauka A Indonesia Domin Ziyarar Aiki

May 24, 2025
Tawagar MDD Da Majalisar Shugabancin Libya Sun Kafa Kwamitin Tsagaita Bude Wuta

Tawagar MDD Da Majalisar Shugabancin Libya Sun Kafa Kwamitin Tsagaita Bude Wuta

May 24, 2025
Firaministan Sin Ya Shugabanci Taro Kan Masana’antu Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Da Kare Muhalli 

Firaministan Sin Ya Shugabanci Taro Kan Masana’antu Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Da Kare Muhalli 

May 24, 2025
Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF

Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF

May 24, 2025
CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari

CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari

May 24, 2025

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

May 24, 2025
Sin Ta Jaddada Da Muhimmancin Tsagaita Bude Wuta A Zirin Gaza

Sin Ta Jaddada Da Muhimmancin Tsagaita Bude Wuta A Zirin Gaza

May 24, 2025
An Kaddamar Da Bikin Baje Kolin Aikin Gona Na Kasa Da Kasa Na Cote d’Ivoire

An Kaddamar Da Bikin Baje Kolin Aikin Gona Na Kasa Da Kasa Na Cote d’Ivoire

May 24, 2025
Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 

Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 

May 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.