Rahoton UNICEF ya bayyana cewa yara sama da 536,000 ba sa zuwa makaranta a Jihar Katsina, wanda ke nuna matsalar ilimi na ƙara ƙamari a yankin. Wannan al’ƙalumman sun fito ne daga bakin shugaban ofishin UNICEF na Kano, Rahama Mohammed Farah, yayin bikin ranar ilimi ta duniya (IDE) 2025.
Farah ta ce matsalar rashin zuwa makaranta a Katsina ta samo asali ne daga baƙin talauci, da ɗabi’u na al’ada, da rashin ingantattun abubuwa isassu a makarantu. Ta kuma bayyana cewa yaran da ke makaranta ma ba sa samun sakamakon karatu mai kyau, inda kashi 26% ne kawai ke iya karatu, yayin da kashi 25% ke da ƙwarewar lissafi na farko.
- UNICEF Ta Nemi Dala Miliyan 250 Don Tallafa Wa Yara A Sakkwato, Zamfara Da Katsina
- Gwamnatin Kano Ta Raba Kayan Makaranta Kyauta Ga Dalibai 789,000
UNICEF ta sanar da matakan da take ɗauka, wanda suka haɗa da tallafawa iyalai, da gyaran makarantu, da horar da malamai, da gina wuraren karatu da ke jurewa yanayin sauyin yanayi.
Har ila yau, ta buƙaci gwamnatin Katsina ta ƙara kashe kuɗi kan ilimi da tabbatar da bayar da kasafin kuɗi akan lokaci don ceto makomar matasa a jihar.