Jaridar The Washington Post ta Amurka ta ba da labari a kwanan baya cewa, tun daga ranar 7 ga Oktoban shekarar 2023, ‘yan Gaza fiye da 60,000 sun halaka sakamakon rikicin da ya barke, cikinsu fiye da 18500 yara ne. Jaridar ta buga jerin sunayen wasu yara daga cikinsu a shafinta, inda suka mamaye shafin baki daya.
Wadannan sunaye ba alkaluma ba ne kawai, suna tattare da makarantun da aka lalata, asibitoci marasa wutar lantarki, da iyalan da ba su da abinci—yaran Gaza, ana kashe su ta hanyar yaki da kuma shingen da aka yi musu.
- Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara
Shugabar UNICEF Catherine Russell ta bayyana a zaman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Tun daga Oktoban 2023, a cikin kowane sa’a fiye da yaro daya yana mutuwa.” Wannan yana nufin cewa yayin da kuke karanta wannan zane da rubutuna, kila karin wani yaro marar laifi a Gaza, ya rufe idanunsa har abada, wasu daga cikin yaran har ba su fara tafiya ba tukuna.
“Jerin sunayen yaran Gaza da ke mutuwa “, dole ne a tabbatar da ba a kara yawansu ba. Shin wadannan sunayen yara kanana da hotunan su ba za su iya tada hankalin bangarori masu rikici ba?
Akasarin kasashen duniya sun yarda cewa “shawarar samar da kasashe biyu” ita ce mafitar warware matsalar Falasdinu, kuma amincewa da kasar Falasdinu wani muhimmin mataki ne na aiwatar da wannan shawara. Kwanan nan, an gudanar da babban taron kasa da kasa kan warware matsalar Falasdinu da aiwatar da shawarar “samar da kasashe biyu” a hedkwatar MDD da ke birnin New York, inda ministocin harkokin wajen kasashe 15 suka sanya hannu kan sanarwar hadin gwiwa, suna nuna niyyar amincewa da kasar Falasdinu. A yanzu, fiye da kashi biyu bisa uku na kasashe membobin MDD sun amince da kasar Falasdinu. Muna fatan ganin an tabbatar da shawarar “kafa kasashe biyu” da wuri, domin hasken zaman lafiya ya zo Gaza. Yaran Gaza ma yara ne, kamar kowane yaro na kowane iyali a duniya, suna da hakkin rungumar gobe. (Mai zane da rubutu:MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp