Rahotonni na nuna cewa Yariman mai jiran gadon mulkin Saudiyya Mohammed Bin Salman, ba zai halarci jana’izar Sarauniya da za a gudanar gobe ba.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wata majiya daga ofishin harkokin kasashen wajen Birtaniya na bayyana hakan.
Matakin da fadar Buckingham ta dauka na gayyatar yariman ya janyo ce-ce-ku-ce daga kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil-adama. Kamar yadda BBC Hausa ya rahoto.
Wani rahoto da hukumar leken asirin Amurka CIA ta fitar ya nuna cewa Yariman na Saudiyya na da hannu a kisa tare da daddatsa gawar ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya a 2018.
Budurwar Jamal Khashoggi, Hatice Gengiz, ta ce gayyatar Yariman ka iya zama wani tabo ga Sarauniya Elizabeth II.