Dan marigayiya Sarauniya Elizabeth II, Yarima Charles ya zama sabon Sarkin Ingila.
Ana sa ran tsohon yariman Wales zai yi jawabi ga al’ummar kasar a yayin da duniya ke alhinin rasuwar sarauniyar da ta fi dadewa kan karagar mulki.
- Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azama Kan Masana’antu Wajen Yin Kirkire-kirkire
- Da Dumi-Dumi: Sarauniyar Ingila, Elizabeth Ta Rasu
Yaran Sarauniya Elizabeth, tare da Yarima William da Yarima Harry, sun ci gaba da kasancewa tare da marigayiyar a Balmoral bayan likitocin sun nuna damuwa game da lafiyarta.
Amma, ta mutu sa’o’i kadan bayan danginta sun kewaye ta.
Bayan rasuwar Sarauniyar, Biritaniya da kasashen Commonwealth za su yi zaman makoki na kwanaki goma yayin da miliyoyin al’ummarta a Birtaniya da kasashen ketare ke jimamin rasuwarta.
Yarima Charles, ya hau karagar mulki zai yi bikin cika shekaru 70 na mulkinta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp