Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta rasu da yammacin ranar Alhamis, bayan fama da rashin lafiya, ta mutu tana da shekara 96 a duniya.
Ta rasu ne bayan ta shafe shekaru 70 a kan mulki.
Iyalanta sun taru a fadarta da ke Scotland bayan an rika nuna damuwa game da yanayin koshin lafiyarta ranar Alhamis.
Sarauniyar Ingila ta hau kan mulki ne a 1952 kuma ta ga sauye-sauye da dama.
Babban danta Charles, tsohon Yarima na Wales, ne zai jagoranci kasar wajen jimami a matsayinsa na sabon Sarki da kuma shugaban kasashe 14 na kungiyar Commonwealth.
A wata sanarwa, Mai Martaba sabon Sarki ya ce: “Mutuwar mahaifiyata abar kaunata Mai Martaba Sarauniya, lokaci ne na matukar bakin ciki a gare ni da dukkan iyalaina.
“Muna matukar jimamin rasuwar Basarakiya abar bege kuma mahaifiyata abar kaunata. Na sani cewa rashinta zai matukar yi wa ‘yan kasar nan da Commonwealth zafi.”
Ya kara da cewa a yayin da suke jimamin rasuwarta da kuma sauyin da aka samu, shi da iyalansa za su “nutsuwa da kwanciyar hankali ne bisa sanin cewa duk fadin duniya ana girmamawa da kuma kaunar Sarauniya”.