Yarima Monaco Albert Alexandre Louis Pierre Grimaldi yana da daddaden zumunci da shugaban kasar Sin Xi Jinping, sun taba ganawa da juna sau da dama.
A ran 24 ga watan Maris na shekarar 2019, Xi Jinping, wato shugaban kolin kasar Sin na farko da ya kai ziyarar aiki a Monaco. Yarima Albert na II ya alamta wannan ziyara a matsayin abin farin ciki matuka, duba da cewa, shi ne karo na farko ne shugaban kasar wadda ke da matukar tasiri a duniya, ya kai ziyara a kasarsa.
- Buhun Taki Miliyan 2 Da Biliyan 100 Da CBN Ya Bayar Zai Daidaita Farashin Abinci -Kyari
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 3 Da Ake Zargi Da Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane A Bauchi
Xi Jinping da Yarima Albert na II suna da sha’awa iri daya a mabambanta bangarori. Dukkansu sun taba halartar bukukuwan kaddamar da gasar Olympic ta lokacin hunturu da aka gudanar a Sochi, da gasar Olympic ta matasa ta Nanjing da bikin bude gasar Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing. A cewar Yarima Albert na II, Xi Jinping ya fahimci muhimmancin wasan motsa jiki matuka, saboda ba ma kawai ya goyi bayan karbar bakuncin shirya gasar Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing na shekarar 2022 ba, har ma ya yi fatan al’ummar Sin su motsa jiki.
Sau da dama Xi Jinping ya nanata cewa, zamanintar da al’ummar kasar Sin aiki ne na raya bil Adam da sauran hallitu gaba daya. A cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin na nuna himma da kwazo wajen kaddamar da manyan ayyukan kiyaye kasancewar halittu iri-iri da yawa. Matakin da ya amfanar da wasu hallitu dake cikin hadarin bacewa sosai. Kuma abin ya jawo hankalin Yarima Albert na II, wanda shi ma yana mai da hankali kan wannan aiki. Ya ce, “Abin da ya fi burge ni shi ne, alkawari da niyyar Xi Jinping da gwamnatinsa na kiyaye muhalli. Ina matukar fahimtar shawarar kafa makomar bil Adam ta bai daya. A ganina, mai da hankali kan makomar bil Adam shawara ce ta na-gari. (Amina Xu)