Wata yarinya mai shekara 14 a Jihar Jigawa, ta amsa laifin zuba wa mijinta da abokansa guba a abinci, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaya daga cikin abokan mijin.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Bakata da le ƙaramar hukumar Kiyawa, a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamban 2024.
- Awannin Da Sallamarsu A Matsayin Kwamishinoni, Gwamnan Bauchi Ya Naɗa 3 A Matsayin Mashawarta
- Ana Kara Zuba Jarin Waje A Kasar Sin A Sabuwar Shekara
Yarinyar ta saka gubar a taliya, inda nan take mijinta da abokansa suka fita hayyacinsu.
An garzaya da su asibitin Jahun, amma ɗaya daga cikin abokan ya mutu.
Yarinyar ta ce tsohon saurayinta, wanda ɗan uwanta ne, ya ba ta gubar.
Sai dai shi ya musanta zargin, yana cewa ba ya cikin garin lokacin da abin ya faru.
Yanzu haka, yarinyar tana hannun ‘yansanda, yayin da tsohon saurayin ke tsare a gidan yari.
Alƙalin da ke sauraron shari’ar, ya ɗage ƙarar zuwa 17 ga watan Fabrairun 2025.