A dai-dai lokacin da jam’iyyu a Nijeriya ke ƙoƙarin kammala zaɓukan fidda gwani domin miƙawa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC sunayen waɗanda za su shiga babban zaɓen shekarar 2023.
Zamu ɗan yi taƙaitaccen nazari akan makomar siyasar ɗan majalisar wakilai mai wakilatar ƙaramar hukumar Birnin Kano a zauren majalisar wakilai, Sha’aban Ibrahim Sharada.
- Zaben APC: Ragowar ‘Yan Takara Sun Yi Watsi Da Matakin Gwamnoni Na Ware Mutum 5
- Gwamnonin APC Sun Kara Rage Adadin ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Daga 5 Zuwa 3
Sha’aban Ibrahim Sharada ya kasance ƙalilan daga cikin matasa a jihar Kano da su ka samu babbar dama a siyasa irin ta Najeriya, musamman idan aka yi la’akari da ƙananan shekarunsa da kuma muƙamin da ya fara da shi wato mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin watsa labarai wanda wannan ce ta ba shi damar samun takarar ɗan majalisar wakilai kuma ya yi nasara a zaɓen shekarar 2019, duk da irin ƙalubalen da ya fuskanta a cikin jam’iyyar APC reshen ƙaramar hukumar Birni.
Samun wannan nasara da Sha’aban ya yi ta sa ya samu damar kasancewa shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan Najeriya. Tabbas wannan matashin ɗan siyasa ya samu dama fiye da wasu daga cikin takwarorinsa musamman waɗanda su ka fito daga jihar Kano.
Kamar yadda al’umma ke yiwa siyasar Kano kirari da cewa ‘Siyasar Kano Sai Kano’, wannan babu shakka haka abin ya ke domin sunan Sha’aban Sharada ya karaɗe da’irar siyasar Kano, musamman a shirye-shiryen siyasa da ake gabatarwa a jihar.
Duk da irin rikicin siyasar da ke tsakanin Sha’aban da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Kwamishina Mukhtar Ishaq Yakasai da tsohon ɗan majalisar dokoki Dakta Baffa Babba Danagundi da shugaban ƙaramar hukumar Birni, Fa’izu Alfindiki, amma hakan bai sa gwiwar matashin ɗan siyasar ta yi sanyi a siyasance ba, domin tuni ya cika kafafen yaɗa labarai akan bayyana buƙatarsa ta yin takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC ba.
Irin ƙarfin hali da kuma tsiwar da Sha’aban ɗin ke yiwa jiga – jigan jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Birnin Kano, ya sanya ake masa laƙabi da SAURO Mai Hana Giwa Bacci. Kuma ga duk mai bibiyar siyasar Kano, ya ga matashin ɗan siyasar ya tayar da ƙura a cikin jam’iyyar APC, musamman a lokacin da ake shari’a mai nasaba da shugabanci a jam’iyyar.
Tabbas irin yadda kafafen yaɗa labarai na ciki da wajen Najeriya, su ka baiwa Sha’aban haɗin kai da kuma rawaito irin nasarar da tsaginsu na G7 ke samu akan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya ya ke ganin babu wani ɗan siyasa a gabansa a cikin jam’iyyar APC.
A ɗaya ɓangaren kuma Sha’aban ɗin ya tattara wasu matasa a cikin wata ƙungiya mai suna FITILAR Kano, da babban aikinsu shi ne kare muradinsa da kuma ganin bukatar sa ta biya ta hanyar tattara masa matasa da ba su horo kan ƙananan sana’o’in dogaro da kai a wasu daga cikin ƙananan hukumomi 44 da ke Kano.
Jami’yyar APC tana fara sayar da fom ɗin takara a dukkanin muƙamai, sai aka jiyo wata gamayyar ƙungiyar matasan da Sha’aban ɗin ya samawa shirin nan na gwamnatin tarayya mai laƙabin N- POWER, sun tara kuɗi kimanin Naira Miliyan 50 tare da siyawa Sauro ɗin fom ɗin takarar gwamnan Kano.
Wannan ce ta ba shi damar shiga zaɓen fidda gwani tsakaninsa da mataimakin gwamnan Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, inda Sha’aban Ibrahim Sharada, ya yi rashin nasara, wanda hakan ne ya bai wa tsohon Kwamishinan Ayyuka na musamman, Muntari Ishaq Yakasai damar samun tikitin takarar majalisar wakilai ta tarayya, a ƙarƙashin jam’iyya APC.
Gabanin fara zaɓen fidda gwanin Sha’aban Ibrahim Sharada ya gabatar da wani jawabi na mintuna 12 a gaban gwamna Abdullahi Umar Ganduje da duk wani mai ruwa da tsaki na jam’iyyar APC reshen jihar Kano, inda a nan aka ji Sauro ɗin ya tuba daga dukkanin irin tsiwar da ya yiwa manyan jam’iyyar tun daga kan Gwamna har zuwa kan shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, Fa’izu Alfindiki, tare kuma da sha alwashi akan zai karɓi sakamakon zaben fidda gwanin.
Sai dai wani abu mai kama da tufka da warwara da Sauro ɗin shi ne yadda aka jiyo shi ya ki amincewa da sakamakon zaben tare da rubutawa uwar jami’yyar ta ƙasa ƙorafi tare kuma da zargin da ɗan majalisar ya yi akan cewa an kashe masa magoya baya tare da jikkata waɗansu, sai dai jami’an ƴan sanda a Kano sun shaida wa manema labarai cewa babu rahoton rikici a yayin zaben balle a yi maganar hare-hare ko asarar rai, har aka kammala zaben.
Yanzu abin tambayar shi ne; Mecece makomar siyasar Sha’aban Ibrahim Sharada ɗin a fagen siyasar Kano? Ko zancen ƴan duniya ya ɗebi Sauro ya wuce matsayinsa?