A kwanakin nan, maganar Taiwan ta sake janyo hankalin mutanen duniya, sakamakon yadda wata babbar jami’ar kasar Amurka ta kai ziyara a yankin Taiwan na kasar Sin, duk da rashin amincewa da gargadi da gwamnatin kasar Sin ta yi, lamarin da ya tilasta wa Sin daukar wasu matakai, ciki har da atisayen soja a kewayen tsibirin Taiwan.
Duk lokacin da aka ambaci Taiwan ya kan sa ni tunawa da wani batun da ya faru a baya: Wata rana, na je ajiye kudi a wani banki a birnin Ikko na Najeriya. Ina jira a zo kaina, sai wani ma’aikacin banki ya taimaye ni, “Me ya sa kasar Sin ba ta yarda da ‘yancin kan Taiwan ba?”.
Maimakon na amsa tambayarsa, sai ni ma na yi masa tambaya: “Me ya sa Najeriya ba ta yarda da ‘yancin kan Biafra ba?” Ma’aikacin ya rasa abin da zai fada.
Wasu kafofin yada labaru da ‘yan siyasa na kasashen yamma suna son kwatanta Taiwan da Ukraine, amma hakika akwai bambanci tsakaninsu.
Ukraine wata kasa ce, yayin da Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. Kasar Sin ba za ta yarda da ‘yancin kan Taiwan ba, kamar yadda ita ma gwamnatin Najeriya ba za ta taba amincewa da ballewar yankin kudu maso gabashin kasar, da kafuwar “jamhuriyar Biafra” ba.
Duk wanda ya ke karanta labarun abubuwan dake faruwa a sassan duniya, tabbas ya taba jin manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Ma’anar wannan manufa ita ce: Kasar Sin daya ce tak a duniyarmu, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya balle shi ba, kana gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin, ita ce halaltacciyar gwamnati daya tak da take wakiltar daukacin al’ummun Sin.
Wannan manufa ita ce tushen kulla huldar diplomasiya tare da kasar Sin, kana wata babbar ka’ida ce da Majalisar Dinkin Duniya da gamayyar kasa da kasa suke amincewa da ita.
Saboda dukkan kasashen da suka kulla huldar diplomasiya tare da kasar Sin sun yin alkawarin girmama manufar kasancewar kasar Sin daya tak, sa’an nan galibin kasashen duniya sun riga sun kulla hulda da Sin. Don haka, idan kowace kasa ta iya cika alkawarin da ta yi, to, ba za a samu maganar Taiwan ba.
Amma abin takaici shi ne, akwai kasar da ta yi amai ta lashe kan wannan manufa.
Babban dalilin da ya haddasa maganar Taiwan shi ne kasar Amurka. Da ma a shekarar 1949, Sinawa sun kawo karshen yakin basasa na kasar na shekaru 3, tare da kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
A lokacin, wasu sojoji da jami’ai na jam’iyyar Kuomintang sun gudu zuwa tsibirin Taiwan na kasar, inda suka mallaki tsibirin bisa goyon bayan gwamnatin kasar Amurka.
Daga bisani, Amurka ta fara yin amfani da maganar Taiwan wajen neman shawo kan kasar Sin: Idan tana neman samun goyon bayan kasar Sin, sai ta dan nisanta kanta da bangaren Taiwan.
Amma idan tana so ta matsawa kasar Sin lamba, to, sai ta bijiro da maganar baiwa yankin Taiwan tallafin makamai, da nuna goyon baya ga masu neman ‘yancin kan Taiwan a asirce, ko kuma sanya wasu manyan jami’anta kai ziyara yankin Taiwan, da dai sauransu.
Sanin kowa ne cewa, Amurka ta kwashe fiye da shekaru 70 tana yin haka, shin za ta iya kiyaye yanayin a wannan zamanin da muke ciki? Bayan da Nancy Pelosi, babbar jami’a mai matsayi na uku a gwamnatin kasar Amurka, ta ziyarci yankin Taiwan a wannan karo, rundunar sojojin kasar Sin ta kaddamar da babban atisayen soja a kewayen Taiwan, wanda ba a taba ganin irinsa ba a baya.
Hakan ya shaida karfin kasar a fannin dinke kasa ta matakan soja. Sai dai za ta ci gaba da neman dinkuwar kasa waje guda ta hanyar lumana. Sinawa suna da cikakken imani kan makomar lamarin.
A ganinsu, abin da ya faru sakamakon yadda al’ummar kasar ba su da karfi a baya, za a iya daidaita shi, bayan da kasar ta samu ci gaba, da farfadowar al’ummarta.
A ganin Sinawa, yankin Taiwan tamkar wani yaro da ya bar gida, ya tafi bulaguro a waje, kuma tabbas wata rana zai koma gida. (Bello Wang)