Yau Lahadi da misalin karfe 5 na yamma manyan kungiyoyin kwallon kafa da ke buga gasar Firimiya Lig ta kasar Ingila, Manchester United da Manchester City za su hadu a babban filin wasa na Etihad Stadium dake Manchester domin wasan mako na 16.
Wasa a tsakanin kungiyoyin biyu na daga cikin manyan wasannin kwallon kafa da ke matukar kayatar da masu sha’awar kwallon kafa a fadin Duniya,saboda duka biyun babu kanwar lasa a cikinsu matukar ana maganar taka leda.
- ASUU Ta Fara Gangamin Shiga Yajin Aiki Yayin Da Gwamnatin Tarayya Ta Kasa Cika Alkawari
- Nijeriya Za Ta Shiga Cikin Manyan Kasashe Masu Fitar Da Amfanin Gona A 2025 – Tinubu
Wasan na yau shi ne wasa na 192 da suka hadu da juna, Manchester United ce kan gaba a wajen samun nasara inda ta samu nasarori sau 78 aka buga canjaras 53 yayinda Manchester City ta samu nasara sau 60.
Sabon kocin Manchester United Ruben Amorim na fatan ganin samun nasara a karon farko na wasan Manchester Derby yayinda Pep Guardiola na Manchester City ke fatan ganin kungiyar ta dawo cikin ganiyarta bayan rashin nasarori da ta ke fama dasu a yan kwanakinnan.