A yau Litinin Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya za ta soma tantance masu neman takarar shugaban ƙasa inda ake sa ran kai har gobe Talata ana gudanar da tantancewar.
BBC Hausa, ta rawaito cewa, Jumullar mutum 23 ne ake sa ran cewa za su halarci tantancewar.
Rahotanni na cewa ana sa ran tantance mutum 11 a yau Litinin, sa’annan kuma sauran 12 kuma a gobe Talata.
Wannan duk na zuwa ne bayan da jam’iyar ta APC ta ɗage zaɓen fitar da gwanin da ya kamata ta gudanar 29 da 30 ga watan Mayu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp