A yau Litinin ne zaman kotun sharia’r mawaki G-fresh da matarsa ta farko Sayyada Sadiya Haruna mai maganin mata,inda kotun dake zamanta a filin hoki dake Zoo road kano zata gudanar da shariar da misalin karfe 9:00 na safiya kamar yadda mawakin ya bayyana.
Dambarwa dai ta barke ne tsakanin G-fresh da Matarsa Sadiya bayan makonni kadan da yin auren su biyo bayan zargin da G-fresh yayi cewa ya kama wani gardi a gidan matar tasa.
- Abba Gida-Gida Ya Nada Sunusi Oscar A Matsayin Mataimakinsa Akan Masana’antar Kannywood.Â
- Na Kusa Yin Aure Nan Da Dan Lokaci Kadan — Rahama Sadau
Yanzu dai Sadiya ta bayyana cewa mijin nata ya sake ta, lamarin da shi G-fresh ya musanta tare da bayyana cewa har yanzu matarsa ce domin bai sake ta ba.
Ita kuma Sayyada Sadiya Haruna ta dauki matakin kai maganr gaban sharia’ domin warware dambarwan auren nasu.