Yau Lahadi, manyan kungiyoyin Manchester dake buga gasar Firimiya Lig ta kasar Ingila – Manchester United da Manchester City zasu kara a wasan mako na 31 na Firimiyar bana.
Manchester City da ta lashe kofin a bara, ta na matsayi na 5 da maki 51, maki 22 kenan tsakaninta da Liverpool dake matsayi na 1 akan teburin gasar.
Manchester United kuma wannan kakar ba ta zo mata da dadi ba, inda yanzu haka ta ke a matsayi na 14 da maki 37 a wasanni 30 da ta buga.
Kungiyoyin biyu sun hadu sau 193 a tarihi, Manchester United ke kan gaba a samun nasarori, inda ta samu nasara sau 79 akayi canjaras 54 yayinda City ta doke United sau 60.
Wasan na yau, Lahadi 6 ga watan Afrilun, 2025 za a fara ne da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp