• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaushe Ne Za A Ga Bayan Hare-haren Bindiga A Kasar Amurka?

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

Yayin da ake dab da fara bikin gargajiya a kasar Amurka wato ThanksGiving Day, an sake samun harbe-harben bindiga a kasar.

A ranar 22 ga wata, agogon wurin, harin bindiga da ya auku a wani kantin zamani da ke birnin Chesapeake na jihar Virginia, ya yi sanadin mutuwar mutane shida, tare da jikkatar wasu hudu. Kwanaki uku kafin wannan hari, wani harin bindiga da ya auku a birnin Springs na jihar Colorado ya halaka mutane biyar, tare da jikkata wasu 25.

  • An Yi Ganawa Tsakanin Ministocin Tsaron Kasashen Sin Da Amurka 

Ranar ThanksGiving biki ne na haduwar iyali, amma hakan ba zai yiwu ba ga iyalai da dama sakamakon hare-haren bindigar dake faruwa.

Ba da jimawa ba ne, wani hoton bidiyo ya karade shafin yanar gizo, inda ake ganin wata ’yar Amurka ta saya wa danta mai shekaru 5 da haihuwa wata jakar makaranta da za ta iya kare shi daga harbin bindiga, tare da horar da shi a gida kan yadda zai iya gudu daga hare-haren bindiga. Wadanda suka kalli bidiyon da dama sun ce, hakan abin bakin ciki ne. Babu shakka, sai dai gaskiyar lamarin da ya faru ya fi hakan bakin ciki, idan ba a manta ba, a ranar 24 ga watan Mayun bana, harin bindiga da ya faru a makarantar firamare ta Robb, ya yi sanadin mutuwar yara 19 da ma malamai 2, lamarin da ya jawo suka daga bangarori daban daban kan rashin daukar matakan shawo kan matsalar da gwamnati ta yi.

Alkaluman da shafin yanar gizo dake bayani game da matsalar harbin bindiga mai suna “Gun Violence Archive” ya fitar, sun yi nuni da cewa, tun farkon bana har zuwa ranar 21 ga watan Nuwamba, mutane sama da dubu 39 sun mutu sakamakon hare-haren bindiga a kasar ta Amurka, kuma shekaru uku a jere yawan harbe-harben bindiga da suka faru a duk shekara ya wuce 600 a kasar.

LABARAI MASU NASABA

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

Yara manyan gobe, abin kunya ne yadda kasar ta Amurka ta kasa kare yaranta daga hare-haren bindiga. Rayuka su ne tushen hakkin dan Adam, kuma abin takaici ne yadda hare-haren bindiga suke ta halaka ’yan kasar. (Mai Zane: Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka
Daga Birnin Sin

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

October 18, 2025
Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Next Post
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 5, Sun Kama Wani Guda Daya

Sojoji Sun Kashe 'Yan Boko Haram 5, Sun Kama Wani Guda Daya

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

October 18, 2025
JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.