An yi tattaunawa kan batun kare hakkin bil adama tsakanin kasar Sin da Tarayyar Turai (EU) jiya Litinin a birnin Beijing, inda mashawarcin ministan harkokin wajen Sin Miao Deyu, ya bayyana matsayin kasar Sin da ra’ayinta kan batun kare hakkin bil adama.
Yayin tattaunawarsa da mataimakiyar babban direktan hedkwatar sashen Asiya da Pacific ta hukumar gudanarwar EU Paola Pampaloni, ya kuma bayyana ci gaban da Sin ta samu game da batun, tare da nanata niyyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin wajen bautawa al’umma.
- Jirgin Kasa Mai Saurin Tafiya Da Ya Hada Babban Yankin Sin Da Hong kong Ya Fara Aiki
- Ya Kamata Amurka Ta Cire Cuba Daga Jerin “Kasashe Masu Goyon Bayan Ta’addanci”
Kare hakkin bil adama a ganina shi ne, kasancewar al’umma cikin yanayi na walwala da wadata da tsaro da ci gaba ta kowacce fuska. A duniyar yanzu, da an ambaci kasar Sin, abun da za a tuna shi ne, ci gaban da kasar ta samu ta fuskoki da dama, kuma wannan ba ci gaba ne na fatar baki ba, abu ne da ake gani a aikace, kuma a zahiri, wadanda al’ummar kasar ke mora. Duk wani abu da gwamnatin Sin za ta yi, to abu na farko da ta kan yi la’akari da shi, shi ne moriya da bukatu da muradun jama’arta.
Na kan yi mamaki idan aka ce wai kasar Sin na keta hakkokin bil adama. Shin yaushe tabbatar da tsaron al’umma ya zama keta hakkin bil adama? Yaushe yaki da ta’addanci ya zama keta hakkin bil adama? Yaushe kuma kokarin tabbatar da dunkulewar yankunan kasa ya zama take hakkin bil adama? Idan muka yi nazari, za mu iya fahimta cewa, dukkan abubuwan da ake fakewa da su wajen shafawa kasar bakin fenti, abubuwa ne da za su iya haifar da rikici ko koma baya ga kasar, idan har ba ta dauki matakai masu kwari kamar yadda take yi ba.
Har kullum na kan jinjinawa irin matakan da Sin ke dauka na tabbatar da tsaro da kare moriyarta da ta jama’arta, kasancewar na ga illar ayyukan ta’addanci a zahiri. A ganina da dukkan kasashe za su yi koyi da irin dabarun kasar Sin na jajircewa, to, da duniya ba ta shiga cikin yanayin da take ciki ba.
Tabbas Sin ta samu ci gaba a bangaren kare hakkin bil adama, domin al’ummarta na cikin kwanciyar hankali da wadata da more rayuwa mai dadi. Ya zama wajibi kasancen yamma su gane cewa, dabaru ko matakansu, ba su ne kadai mafita ba. Haka kuma, ya dace su sakarwa Sin mara ta ci gaba da zabarwa kanta hanyar da ta dace na tafiyar da harkokinta na cikin gida ba tare da sun yi katsalandan ba.