Har sai yaushe ne za a kawo karshen wannan karancin man? tambayar da ke bakin kusan dukkan ‘yan Nijeriya ke nan a ‘yan kwanakin nan. Nijeriya na fuskantar matsanancin karaci da tsadar man fetur, abin da ke tsayar da harkokin zirga-zirga da kasuwanci cik a wasu sassan kasa, ya kuma haifar da tsadar kayayyakin masarufi da al’murran yau da kullum, wannan kuma ya sa al’umma tunanin gaskiyar ko janye tallafin man fetur da aka cewar zai kai ga magance matsalolin da ake fuskanta tattare da albarkatun man fetur a Nijeriya za a kai ga ganin karshensu ko dai abin ya zama labari ke nan kawai?.
A ranar 29 ga watan Mayu 2023 da Shugaban kasa Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur, abin da ya haifar da karin kudin litar fetur nan take.Al’umma sun dauka wannan tashin gwauron zabon shi ne zai kawo mana karshen karancin man fetur din a Nijeriya.
- Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN Ya Dakatar Da Harajin Tsaron Yanar Gizo
- Mun Kawo Jam’iyyar AAC Ne Domin Al’ummar Adamawa – Doubli
Amma sai gashi abin bai kasance haka ba.A makon jiya sai gashi dogayen layukan mai a gidajen man fetur sun bayyana a Abuja da wasu jihohin kasar nan,wanda hakan yake tuna mana halin da aka shiga shekarun baya da aka fuskanci irin wannan matsanancin karancin man fetur a Nijeriya.
Kamfanin kula da albarkatun mai na kasa (NNPCL) ya dora alhakin karancin man a kan kamfanonin masu jigilar man fetur daga wuraren ajiyar mai da ke sassan daban daban na kasar.
Duk da sun bayyana cewa, sun yi maganin matsalar amma a zahiri matsalar na nan har yanzu babu wasu alamun kawo karshen lamarin.
Babu man fetur a gidajen sayar da fetur, kudaden mota sun yi tashin gwauron zabo, takalawa na ci gaba da dandana radadin hauhawar farashin kayan masarufi.
Al’umma ba su gamsu da hujjojin da gwamnati ke bayarwa ba, wadanda suka hada da matsalar zirga-zirga ta masu dakon fetur, fashewar bututun mai, masu satar danyen mai da kuma wai mastalolin da ke fuskanta na karancin kudaden kasashen waje.Wadannan ba sabbin matsaloli ba ne,amma gwamnatotocin da suka gabata da na yanzu duk sun kasa magancewa tare da samar da tabbataciyar hanyar ganin an kawo karshen kwarancin man a fadin tarayyar kasar nan.
A ra’ayinmu, wannan wani abin kunya ne ga kasa,a ce babbar kasa a Afirka kamar Nijeriya da ke a kan gaba a cikin kasashe masu albarkatun man fetur a duniya amma ta kasa samarwa al’ummarta da masana’antunta man da suke bukata ba.Matatun mai 4 da ke Nijeriya sun kasa wadatar da al’umma man da ake bukata, duk kuwa da dimbin kudaden da ake zubawa a duk shekara don gyaransu.
An kasa cika dukkan alkawuran farfado da wadannan manyan kaddarorin kasa. Yayin da matatar mai ta Dangote ke dan ba mu fata, amma hakan ba zai dauke wa gwamnati hakkinta ba na tabbatar da ganin matatun mai na kasa sun dawo suna aiki kamar yadda ya kamata ba, domin al’umma su amfana.
Hasashen da gwamnati ta yi na cewa, matatar mai ta Kaduna zata dawo aiki a karshen shekarar 2024 da kuma cewa, matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki a cikin watan Afrilu na 2024, abu ne da ba za a aminta da shi ba har sai mun gani a kasa.
Hujjar da NNPCL ke bayarwa ta cewa, mastalar dakon mai daga wurin ajiyar mai da ke Legas ta haifar da karancin man, wata alama ce da ke nuna yadda aka dogara da wurin ajiyar mai guda daya wanda ke Legas wannan kuma ai rashin dabara ne.
In har ana son a kawo karshen wannan karancin man, dole ne a farfado da ayyukan wuraren ajiyar mai 21 da ake da su a fadin tarayyar kasa nan,a kuma yi maganin ‘yan ta’adda masu farfasa bututun mai da ke kai man fetur wuraren ajiyar.
Karin abin takaici a nan kuma shi ne akwai yiwuwar wannan karancin man da mu ke fuskanta ya kazance in har kungiyar masu dakon man fetur suka aiwatar da barazanar da suke yi ta shiga yajin aiki saboda rashin biyansu bashin Naira Biliyan 200 da suke bin gwamnati.
Matsalar karancin man fetur ta ta’azara ne sakamakon rashin tsayayyen tsarin gwamnati a kan tafiyar da harkokin man fetur a Nijeriya da kuma yadda ake tara bashin kamfanonin dakon mai ba tare da an biya su ba, uwa uba kuma shi ne karyewar darajar naira da yadda dala ke kara hauhawa.
Duk da cewa, kamfanin mai na NNPCL ya ce yana da ajiyar man fetur fiye da lita biliyan 1.5, tabbas wannaN ba zai yi maganin matsalar da ake ciki ba, tun da ba a yi maganin matsalar ba tun daga tushenta.
Nijeriya na asarar tiriliyoyin naira sakamakon sace danyen mai da kuma yadda ‘yan ta’adda ke fasa bututun mai amma kuma an kasa kamawa tare da hukunta masu aikata wannan danyen aikin.
A yayin da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da dandana radadin karacin man fetur, al’umma na tunani tare da tambayar wai yaushe ne za a kawo karshen wannan karancin man da ake fuskanta?
Gwamnatocin da suka gabata sun yi nasu kokarin na ganin an kawo karshen matsalar da ke tattrare da karancin man fetur amma har yanzu an kasa gano bakin zare. Gwamnatin Bola Ahmed Tijubu ta gaji wannan matsalar ne amma dole ta samar da hanyar kawo karshena, musamman ganin yadda lamarin ya jefa al’ummar Nijeriya cikin halin ni ‘yasu.
Matsalar karancin man fetur ba abin da ya shafi tattalin arziki kadai ba ne amma ya kuma shafi matsalar tsaron da ake fama da si a sassan Nijeriya.Kasar da ba za ta iya samarwa masa’anantunta, bangaren sufuri man fetur na gudanar da ayyukanta ba tabbas ta shiga halin takura wanda zai haifar mata da koma baya a dukkan harkokin ci gabanta, al’ummarta kuma za su ci gaba da dauwama a cikin kangin talauci.