Yau ce ranar dasa bishiyoyi ta kasar Sin, kuma albarkacin ranar ofishin kwamiti mai kula da harkokin dasa bishiyoyi na Sin ya gabatar da sanarwar karuwar yawan bishiyoyi da Sin ta dasa, wadda ta nuna cewa, Sin ta gabatar da manyan tsare-tsaren kiyaye muhalli, don daidaita harkoki masu nasaba da hakan a shekarar 2024, inda aka samu ci gaba mai armashi a bangaren dasa bishiyoyi.
Sanarwar ta nuna cewa, a wannan shekara Sin ta dasa itatuwa hekta miliyan 4.446, da ciyayi hekta miliyan 3.224, da kuma daidaita kasa mai rairayi hekta miliyan 2.783, hakan ya sa yawan fadin gandun daji ya kai kashi 25%.
Tun lokacin da aka kira taro karo na 18 na jam’iyyar JKS, hukumar lura da itatuwa da ciyayi ta Sin ta aiwatar da manyan ayyukan dasa bishiyoyi da habaka fadin gandun daji, da kyautata ingancin itatuwa da kiyaye albakatun bishiyoyi. Yawan itatuwa da Sin ta dasa a wurare masara shuke-shuke ya kai hekta miliyan 77.33, hakan ya sa Sin ta zama kasa mafi samun ci gaba wajen dasa bishiyoyi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp