Hukumar lura da hada hadar musayar kudaden waje ta kasar Sin, ta ce yawan cinikayyar waje ta Sin a fannin hajoji da bayar da hidimomi ya kai kudin Sin kusan yuan tiriliyan 4.18 a watan Agusta, adadin da ya karu da kaso 4 bisa dari kan makamancin lokacin bara.
Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan, sun kuma nuna cewa darajar hajoji da hidimomi da Sin din ke fitarwa zuwa kasashen ketare ya kai dalar Amurka biliyan 322.4, yayin da darajar su da take shigowa da su ya kai dala biliyan 263.5, adadin da ya nuna rarar dala biliyan 58.9. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp