Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da sanarwar bunkasuwar tattalin arziki da al’umma na jamhuriyyar jama’ar kasar Sin a shekarar 2022.
Alkaluman da ta fitar Litinin din nan ya nuna cewa, yawan GDPn na shekarar bara, ya kai fiye da RMB Yuan triliyan 121 da biliyan 20.7, kwatankwacin dalar Amurka kimanin biliyan dubu 17.5, wanda ya karu da kashi 3 cikin dari bisa na shekarar 2021. Yawan kudin shigar kasar ya kai Yuan triliyan 119 da biliyan 721.5, wanda ya karu da kaso 2.8, idan aka kwatanta da na shekarar 2021.
Adadin marasa aikin yi a birane da garuruwan kasar Sin ya kai kaso 5.6 a duk shekara, yayin da wannan jimilla ta kai kaso 5.5 ya zuwa karshen shekarar. (Amina Xu)