A yau Litinin 27 ga Oktoba, kungiyar jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta ba da rahoton bayanan ayyukan jigilar kayayyakin dake bukatar kankara a watannin Yuni da Yuli da Agustan bana. Bayanan na nuna cewa, a karkashin jagorar manufofi da bukatun kasuwa, aikin jigilar kayayyakin dake bukatar kankara ya nuna samun ci gaba mai karfi tare da fadada girman kasuwa.
Bayanan sun nuna cewa, jimillar da aka samu a wannan bangare a wadannan watanni 3 ta kai tan miliyan 117.3, wadda ta karu da kashi 4.72% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. A cikin watanni 3 na farko na wannan shekara, jimillar jigilar abincin dake bukatar kankara ta kai tan miliyan 309.3, wadda ta karu da kashi 4.49%.
Dangane da kudaden shiga, jimillar kudaden shiga na kamfanonin gudanar da ayyukan jigilar abincin dake bukatar kankara a watannin Yuni da Yuli da Agusta ta kai Yuan biliyan 144.97, wato ta zarce dala biliyan 20, wadda ta karu da kashi kashi 3.92%. A cikin watanni 9 na farko na wannan shekara, jimillar kudaden shiga na wadannan kamfanoni ta kai Yuan biliyan 424.91, kwatankwacin abin da ya haura dala biliyan 59 , wanda ya karu da kashi 3.85%. (Amina Xu)














