Yau Talata, hukumar sufuri ta kasar Sin ta ba da rahoton kididdigar bunkasuwar sha’anin zirga-zirga da sufuri a nan kasar Sin a shekarar 2023.
Rahoton ya nuna cewa, a wannan shekara ta 2023 Sin ta kara inganta samar da manyan ababen zirga-zirga, matsakaicin yawan jarin da aka zuba a duk shekara ya kai fiye da Yuan triliyan 3 kwatankwacin dalar Amurka kimanin biliyan 413.5 a cikin shekaru 7 a jere, yayin da wannan adadi ya kai Yuan triliyan 3.9 a shekarar 2023, wato kwatankwancin dalar Amurka kimanin biliyan 537.5, wanda ke nufin yawan kudin da aka zuba a wannan fanni ya kai dalar Amurka kimanin miliyan 1745 a ko wace rana, lamarin da ya kai sabon matsayi a tarihi.
Ban da wannan kuma, tsarin manyan ababen zirga-zirga ya samu kyautatuwa a bara, tsawon sabbin layin dogo mai saurin tafiya da aka shimfida ya kai kilomita 2776, inda adadin a bangaren sabbin hanyoyin motoci masu saurin tafiya ya kai kilomita 6394, tsawon sabbin hanyoyin da aka shimfida a kauyuka ya kai kilomita dubu 188. (Amina Xu)