Nijeriya na gaf da cika burinta na zuwa matakin hako mai ganga miliyan 1.8 a kowace rana, yayin da man da take hakoka ya karu da ganga 177, 000 a kowace rana a watan Janairun 2024.
A cewar bayanan da shafin hukumar kula da man fetur (NUPRC), ta wallafa, samar da danyen mai na Disamban 2023 da Janairun 2024, ya nuna cewa a Disamban 2023 da Janairun 2023 man da aka hako ya tsaya zuwa ganga 1.55 da 1.64 bi da bi.
- Sin Za Ta Kaddamar Da Gangamin Yayata Ci Gaban Mata
- Gwamnan Gombe Ya Nada Ibrahim Na BBC A Matsayin Shugaban Kafar Yada Labarai Na Gombe
Bayanan ya yi nuni da cewa karuwar man da ake hakowa a kowace rana a Nuwamban 2023 da Janairun 2024 ya karu sama da ganga 177,000 a kowace rana.
“Yana da ban sha’awa a lura cewa a watan Janairun 2024 ya zama mafi girma a hako mai tun Janairun 2022. Wannan wani kyakkyawar yunkuri ne na cika burin kasafin 2024 na hako mai ganga miliyan 1.78 a kowace rana,” a cewar hukumar.
Hukumar NUPRC a kokarinta, a watan da ya gabata ta fitar da tsare-tsaren ayyuka na shekara uku (RAP), na sashin mai da iskar gas a Nijeriya, wanda ake da nufin tara mai miliyan 2.6 a kowace rana zuwa shekarar 2026. A cewata, hukumar ta cancanci yabo kan aiwatar da tsarin RAP da yake haifar da sakamako mai kyau.
Matakin yadda ake hako mai a shekarar da ta gabata ya nuni da cewa a kowace rana ana fitar da gangan danyan mai 41,867,775, wanda aka samu cimmawa zuwa watan Oktoba, amma ya garu zuwa 37,508,971 a kowace rana a watan Nuwamba. A wancan lokacin, mafi karancin farashin danyen mai a watan Nuwamban 2023 ya kai dala 82.94 a kowace lita guda.