Bisa labarin da kamfanin samar da man fetur a kan teku na kasar Sin wato CNOOC ya bayar a yau ranar 23 ga wannan wata, an ce, filin rijiyoyin hakar man fetur mafi girma a kan teku mallakar kasar Sin mai suna Suizhong 36-1 ya samar da man fetur fiye da ton miliyan 100, wanda ya kasance filin rijiya na farko a kan teku da ya samar da man fetur fiye da ton miliyan 100 a kasar Sin.
Filin rijiyoyin Suizhong 36-1 wanda ke arewacin mashigin tekun Bohai na kasar Sin, ya fara aiki daga shekarar 1993. A halin yanzu, filin yana da dandalolin hakar man fetur a kan teku guda 24, da rijiyoyi 545, yawan man fetur da yake samarwa a kowace rana ya kai ton 8900, ya kasance filin rijiyoyi mai muhimmanci a yankin samar da man fetur na tekun Bohai mafi samar da man fetur a kasar Sin.
Mataimakin manajan sashen birnin Tianjin na kamfanin CNOOC Zhang Chunsheng ya yi bayani da cewa, samar da man fetur ton miliyan 100 ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da samun isasshen makamashi, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, da kuma biyan bukatun zaman rayuwar jama’a. (Zainab Zhang)