Bisa labarin da ma’aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin ta bayar, a ranar 4 ga wannan wata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a kasar Sin ya kai miliyan 301 da dubu 291 da dari 1, wanda ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a rabin farko na hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin PRC da bikin Zhongqiu ya kai matsayin koli a tarihi, wato ya kai biliyan 1 da miliyan 243, wannan ya shaida cewa, an fi yin zirga-zirga a lokacin hutun.
Game da hanyoyin zirga-zirga a lokacin wannan hutu, an fi zabar hanyoyin mota. Game da yankunan da aka fi sha’awar ziyarta, an fi zabar biranen Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, da Shenzhen wato birane masu ci gaba, da kuma biranen Chengdu, da Xi’an wato biranen da aka fi zuwa yawon shakatawa. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp