Kungiyar sana’o’in samar makamashi ta amfani da makamashin nukiliya ta kasar Sin ta gabatar da takardar bayani kan bunkasuwar karfin makamashin nukiliya na kasar ta shekarar 2024, inda aka yi bayani kan yadda aka gudanar da aikin samar da wutar lantarki ta amfani da makamashin nukiliya, da masana’antu a wannan bangare, da kuma kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sauransu. Rahoton ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, yawan manyan na’urorin samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya da ake harhadawa ya kai 26 a nan kasar Sin, adadin da ya kai sahun gaba a duniya.
Ban da wannan kuma, rahoton ya ce, gwamnatin Sin ta ba da iznin kafa sabbin ayyukan samar da wutar lantarki ta amfani da makamashin nukiliya 5 a shekarar 2023, yayin da ake harhada sabbin na’urorin samar da wutar lantaki ta karfin nukiliya 5. Har ila yau, yawan wutar lantarki da Sin za ta samar, bisa na’urorin da ake harhadawa zai kai KW miliyan 30.3, adadin ya ci gaba da rike da matsayin koli a duniya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp