Yau Litinin ne cibiyar bayanai da sadarwar yanar gizo ko Intanet ta kasar Sin, ta bayar da rahoton yanayin bunkasuwar Intanet karo na 52, wanda a ciki aka bayyana cewa, ya zuwa watan Yunin bana, yawan Sinawa masu amfani da Intanet ya kai biliyan 1 da miliyan 79, adadin da ya kai kashi 76.4 cikin dari na dukkanin al’ummar kasar.
Rahoton ya nuna cewa, a farkon rabin shekarar bana, yawan kudaden dake shafar cinikin yanar gizo ya kai RMB Yuan triliyan 7 da biliyan 160, adadin da ya karu da kashi 13.1 cikin dari bisa makamancin lokacin bara. Daga cikinsu yawan kayayyakin ainihi da aka sayar a yanar gizo ya kai kashi 26.6%. Kaza lika ya zuwa watan Yuni, yawan Sinawa dake saye kayayyaki ta Intanet ya kai miliyan 884. (Amina Xu)