Alkaluman da hukumar kididdga ta kasar Sin ta bayar a yau Jumma’a sun shaida cewa, yawan mutanen kasashen waje da suka shigo babban yankin kasar Sin ba tare da biza ba a bara, ya kai miliyan 20.12, adadin da ya karu da kaso 112.3%.
Bisa ga alkaluman, yawan baki masu yawon shakatawa da suka shigo babban yankin kasar a bara ya kai miliyan 131.9, wanda ya karu da kaso 60.8%, kuma daga cikinsu miliyan 26.94 ’yan kasashen waje ne, sauran kuma sun fito daga yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin. Sa’an nan, kudin da baki masu yawon shakatawa suka kashe ya kai dala biliyan 94.2, wanda ya karu da kaso 77.8%. Ban da haka, yawan mazauna babban yankin kasar Sin da suka fita daga kasar ya kai miliyan 145.89, kuma daga cikinsu miliyan 97.12 sun je yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp