Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi gargaɗin cewa makomar Nijeriya na cikin hatsari saboda yawan yaran da ba sa zuwa makaranta yana ƙaruwa.
Ya ce wannan matsala na iya ƙara tayar da tarzoma da kuma kawo cikas ga zaman lafiya yayin da yawan jama’ar ƙasar ya kusa kai mutum miliyan 400 nan da shekarar 2050.
- Collins Daga BUK Na Dab Da Shiga Kundin ‘Guinness World Record’ Tare Da Goyon Bayan Indomie
- Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Gwamnatin Amurka Ta Tsayar Da Ayyukanta
Yayin buɗe cibiyar kwamfuta ta Bakhita ICT Centre a Sakkwato, Obasanjo ya bayyana cewa sama da yara miliyan 24 a Nijeriya ba sa zuwa makaranta, inda ya bayyana cewa wannan babbar barazana ce.
“Idan ba mu shirya yanzu ba, abin da muke fuskanta yau zai zama kamar wasa idan aka kwatanta da abin da ke tafe,” in ji shi.
Tsohon shugaban wanda ya mulki Nijeriya daga 1999 zuwa 2007 ya buƙaci shugabannin yanzu su fuskanci matsalar da gaskiya da kuma haɗin kai.
Ya ce bambancin Nijeriya na ƙabilu, addinai da al’adu bai kamata a ɗauka a matsayin matsala ba, illa ma ya zama ƙarfin ƙasar.
“Idan aka tafiyar da bambancin nan da kyakkyawan shugabanci, Nijeriya za ta samu girmamawa a duniya,” in ji shi.
Obasanjo ya jaddada cewa ilimi shi ne tushen ci gaba, ba tare da la’akari da ƙabilanci, addini ko al’ada ba.
Ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, da kuma Bishop Matthew Kukah saboda jajircewa wajen haɗa kan jama’a da zuba jari a ilimi.
Bishop Kukah ya bayyana cewa cibiyar da mai bayar da tallafi Afe Babalola ya gina za ta bayar da horo kyauta ga kowa a fannin amfani da kwamfuta, ƙirƙirar manhajoji, da ilimin kimiyyar bayanai (data science).
Sarkin Musulmi kuma ya jinjina wa Obasanjo saboda kiransa na ci gaba da haɗin kan ƙasa, inda ya roƙi ‘yan Nijeriya su guji rarrabuwar kai don su fuskanci matsalar tsaro tare da bunƙasa ci gaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp