An kammala taron baje kolin zuba jari na duniya na Sin karo na 25 (CIFIT) a jiya Alhamis 11 a birnin Xiamen. A yayin taro na wannan karo, an kulla yarjejeniyoyin ayyukan zuba jari guda 1,154, inda jimillar kudin dake kunshe a ciki ta kai kudin Sin Yuan biliyan 644 (kwatankwacin sama da dala biliyan 90.5 ). An kuma fitar da rahotanni masu inganci guda 21.
Taron mai taken “Hadin kai da Sin don zuba jari ta yadda za a samu bunkasa nan gaba,” ya gudana ne a fadin filin baje koli da ya kai murabba’in kilomita 12. An gudanar da ayyukan habaka zuba jari sama da dari, kuma tawagogin kasashe da yankuna fiye da 120 sun halarta, tare da kokarin kirkirar wani babban baje koli na “Zuba jari a Sin” da kuma muhimmin dandali don habaka zuba jari tsakanin bangarorin biyu.
A lokacin taron, an gudanar da tattaunawa tsakanin manyan kamfanoni na duniya, da kuma tattaunawa tsakanin shahararrun kamfanoni masu zaman kansu da manyan kamfanoni dake sahun gaba a duniya guda 500, da kuma ayyukan tallata kasuwanci sama da 30, wanda ya nuna cikakkiyar dama da samun kuzarin “Zuba jari a Sin” a kowane fanni. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp